19 Janairu 2026 - 11:26
Source: Quds
Sojojin Isra'ila Sun Kai Sumamen Kamu Kogin Jordan

Hare-haren sahayoniyawan da ba a taba ganin irinsa ba a kan yankin Al-Khalil a Yammacin Kogin Jordan 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Majiyoyin labarai sun ruwaito cewa sojojin Isra'ila sun kai hari kan al-Khalil da ke Yammacin Kogin Jordan da kuma tsare Falasdinawa dayawa ba a taba gani irinsa ba. 

Rahotanni da aka wallafa sun ce, dakarun Isra'ila sun sanar da dokar hana fita a yankin da kuma yin gagarumin tsarewa da kama 'yan kasar Falasdinu. Dangane da haka, kamfanin dillancin labarai na Quds al-Akhbariya ya ba da rahoton cewa, dakarun Isra'ila masu mamaye sun rufe manyan tituna a wannan hari da ba a taba ganin irinsa ba.

Your Comment

You are replying to: .
captcha